ABNA24 : Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Zarif ya na fadar haka a shafinsa na Instegram.
Ministan ya kara da cewa ya dauki wannan matsayan ne bayan shawara da abokan aikinsa da dama, da samun tabbacin cewa shigarsa takarar shugabancin kasar ba alkhairi ba ne ba kasar.
A jiya Talatace aka fara rijistan ‘yan saiyasa wadanda suka cika sharuddan shiga takarar shugaban kasa a zaben da za’a gudanar a cikin yan makonni masu zuwa a nan kasar Iran.
Mohammad Javad Zarif dai kwararren jami’an diblomasiyya ne wanda ya dade yana wannan aikin. Daga ciki ya taba zama jakadan kasar Iran a MDD daga 2002-2007.
342/